Isa ga babban shafi
Syria

An kashe mutane 51 a birnin da aka kwato daga hannun ISIL a Syria

An kai wa ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Turkiya hari a kusa da birnin Al-bab da ke Syria tare da kashe mutane 51 kwana guda bayan sanar da nasarar kwato birnin daga mayakan ISIL.

Mutane 51 aka kashe a Al-bab bayan da aka kwato birnin daga ikon mayakan ISIL
Mutane 51 aka kashe a Al-bab bayan da aka kwato birnin daga ikon mayakan ISIL REUTERS/Saad Abobrahim
Talla

Kungiyar nan da ke sa’ido kan rikicin Syria ta ce anyi amfani da mota ne wajen kai harin kunar bakin wake a kauyen Susian mai tazarar kilomita 8 da birnin Al-bab, kuma baya ga salwantar da rayuka, akwai mayaka da dama da aka jikkata .
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman sasanta rikicin kasar na fiye da shekaru biyar

Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura ya bukaci wakilan gwamnati da na ‘yan adawa da ke halartar taron sasanta rikicin kasar a Geneva, da su yiwa Allah su dauki matakin kawo karshen yakin.

Akalla mutane sama da 400,000 aka kashe a yakin da ake ci gaba da fafatawa a kasar, yayin da kowanne bangare ke dagewa sai ya samu biyan bukata.

‘Yan adawar Syria dai na bukatar ganin shugaban kasar Bashar al-Assad ya sauka daga mukaminsa ya bawa gwamnatin wucin gadi da za’a kafa ragamar jagorantar kasar, bukatar da gwamnatin Assad ta yi watsi da ita, yayinda a gefe guda kuma Amurka da Turkiya suka janye daga goyon bayan bukatar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.