Isa ga babban shafi
Malaysia

An bani ladan dala 90 don kashe Kim Jong-nam

Wata mata ‘yar asalin kasar Indonesia da aka kama bisa zargin hannu a kisan Kim Jong-nam ta ce an biya ta kwatankwacin dala casa’in na kudin Malaysia  don watsa masa gubar da ta yi sanadiyar rasa ransa.

Kim Jong-nam da aka kashe a Malaysia
Kim Jong-nam da aka kashe a Malaysia Kyodo/via REUTERS
Talla

Matar mai suna Siti Aisya ta ce ta amshi kudin bayan an ba ta umurnin watsa wa Mista Kim sinadari mai guba da sunan wani shiri na barkwanci da ake dauka wa wata tashar Talabijin.

Bincike ya nuna cewar sinadarin mai guba da aka watsa wa Mista Kim wanda dan’uwa shugaban Koriya ta Arewa da suke uba daya ne guba ce da Amurka ta saka a jerin muggan makamai na kare dangi.

Mista Kim Jong-Nam mai shekaru 45 a duniya na kan hanyarsa ta zuwa birnin Macau daga Kuala Lumpur ne a lokacin da al’amarin ya auku a makon da ya gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.