Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Koriya ta arewa ta haramtawa ‘Yan Malaysia fita kasarta

Koriya ta Arewa ta haramatwa ‘Yan kasar Malaysia barin kasar, matakin da ya dada zafafa tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu, tun bayan kisan da aka yi wa Kim Jing-Nam dan uwa ga shugaba Kim Jong-un na Koriya.

Ofishin jekadancin Koriya ta Arewa a Malaysia
Ofishin jekadancin Koriya ta Arewa a Malaysia REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Koriya ta ce ta dauki matakin ne har sai ta tabbatar da lafiyar jami’an diflomasiyanta da ke Malaysia, da ake zargin cewar suna da hannu wajen kisan Kim Jong-Nam

Firaministan Malaysia Najib Razak ya danganta matakin tamkar garkuwa da ‘yan kasarsu a Koriya ta Arewa.

Rahotanni sun ce ‘Yan Malaysia 11 ne Koriya ta hanawa barin kasar.

A nata bangaren Malaysia ta hanawa ‘Yan Koriya ta arewa fita kasar da suka kunshi jami’an diflomasiyar kasar. Rahotanni sun ce mutanen Koriya sun kai sama da 1,000.

Malaysia na zargin cewar wasu jami’an Koriya na da hannu wajen kisan Jong-Nam.

An kashe Jong-Nam ne a makwanni uku da suka gabata bayan wasu mata biyu sun barbada masa sinadari mai guba a fuska a tashar jirgin sama a Kuala Lumpur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.