Isa ga babban shafi
Yemen

An kashe yara 1,500 cikin shekaru biyu a Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara sama da 1,500 aka kashe a cikin shekaru biyu da aka kwashe ana rikici a kasar Yemen, yayin da sama da 2,400 suka jikkata.

Saudiya da kawayenta na taimakawa gwamnatin Yemen yakar 'Yan tawayen Huthi
Saudiya da kawayenta na taimakawa gwamnatin Yemen yakar 'Yan tawayen Huthi SALEH AL-OBEIDI / AFP
Talla

Hukumar UNICEF da ke kula da yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla yara 1,546 aka kasha daga watan Maris na 2016.

Rahoton ya ce maza kimanin 1, 022 aka kashe, mata 478, sannan adadin yara 46 ba a san jinsinsu ba.

Rahoton na UNICEF ya ce akwai yara kimanin 1,572 da aka tursasawa shiga aikin soja.

Gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiya na fada ne da ‘yan tawayen Huthi ‘yan shi’a da ke samun goyon bayan Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.