Isa ga babban shafi
Lebanon

Shugaban Lebanon ya dakatar da aikin majalisa na tsawon wata daya

Shugaban Lebanon Michel Aoun ya dakatar da zaman majalisar dokokin kasar domin hana ‘yan majalisar tsawaita wa’adin aikinsu da karo na uku a daidai lokacin suke shirin gudanar da zaman domin tsawaita wa’adin.

Michel Aoun shugaban Lebanon
Michel Aoun shugaban Lebanon Dalati Nohra/Handout via Reuters
Talla

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta Fitar ta ce an hana zaman majalisar har tsawon wata daya, kafin aiwatar da gyara ga dokokin tafiyar da zabe na kasar.
A tsarin mulkin Lebanon, shugaban kasa na iya dakatar da aikin majalisa na tsawon wata daya

Tun shekara ta 2013 ne wa’adin ‘yan majalisar ya kawo karshe amma take ci gaba da aikinta. A 2014 Majalisar ta tsawaita wa’adinta na tsawon shekaru biyu da watanni bakwai.

‘Yan majalisar na kokarin kare manufofin jam’iyyun siyasarsu musamman a sabuwar dokar zabe da ake son tabbatarwa a kasar.

Lebanon dai ta shafe kusan shekaru uku tana cikin rudanin siyasa kafin zaben Aoun bayan sasantawa tsakanin shugabannin Kiristoci da Sunni da Shi’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.