rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Masar Abdel Fattah al-Sisi ISIL

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shirin gudanar da bukukuwan Easter a Masar

media
Ana shirin soma gudanar da bukukuwan Easter a Masar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Kristoci a sassan Masar sun gudanar da adduo’i da azumi a yau Juma’a don bikin Good Friday, a yayin da kwanakin bukukuwan Easter ke karatowa, tare da juyayin harin ta’addanci da aka kai kan wasu coci biyu a lahadin da ta wuce inda mutane 45 suka mutu.


Gwamnatin Masar dai ta ayyana dokar ta baci sakamakon hare-haren na ranar lahadin data gabatan.

Kazalika an tura sojoji muhimman wurare dake cikin kasar don tabbatar da doka da oda.

Yanzu haka ma’aikatar cikin gidan kasar ta ce an tantance wanda ya kai daya daga cikin wadanda suka kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen 45 a daya daga cikin mujami’un kasar dake a birnin Alexendria.

Masu bincike sun ce yanzu haka suna ci gaba da aiki domin tantance maharin na biyu da ya tarwatsa kansa a garin Tanta kusan a lokaci daya da harin na farko.