Isa ga babban shafi
Turkiya

Erdoghan ya lashe zaben raba gardama

Jam’iyyun adawa biyu a Turkiya sun sha alwashin kalubalantar sakamakon zaben raba gardamar da aka gudanar a yau Lahadi da ya bai wa shugaba Recep Tayyib Erdoghan karin karfin iko.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya lashe zaben raba gardama.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya lashe zaben raba gardama. REUTERS/Osman Orsal
Talla

 

Jam’iyyun CHP da MHP sun yi zargin cewa an tafka magudi a wajen kidayar kuri’un da kuma yadda hukumomin zabe suka amince da wasu takardun zaben da ba’a tantance sahihancinsu ba.

Sai dai a jawabinsa na farko bayan zaben, shugaba Erdoghan ya jinjinawa al’ummar kasar a rawar da suka taka na bayyana ra’ayoyinsu inda yace sun kafa tarihi sun kuma bude sabon babi a Demokradiyar Turkiya, Erdoghan ya kuma yi kira ga sauran kasashen duniya da su mutunta sakamakon zaben tare da bai wa kasar hadin kai a kokarin da take na yaki da ta’addanci.

Kashi kusan 52 cikin dari daya ne suka amince da bukatar bai wa shugaba Recep Tayyib Erdoghan karin karfin iko.

Da sakamakon wannan zaben raba gardamar shugaban kasar zai soke mukamin firaiminista in har yaso, yana kuma da karfin ikon rusa majalisa idan da bukatar yin hakan  sannan duk wanda ya so ya nada ya nadu.

Sama da mutane miliyan 55 ne dai suka jefa kuriarsu a zaben raba gardamar da aka gudanar a yau Lahadi.

A yanzu haka Shugaba Erdoghan zai sami karfin ikon mulkin kasar fiye da duk wani shugaban Turkiya tun kafuwarta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.