rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi ISIL Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

ISIL ta yi anfani da makami mai guba a Mosul

media
Rundunar sojin Iraki ta ce tana samun galaba akan mayakan ISIL. REUTERS/Stringer

Rundunar Sojan kasar Iraqi ta ce mayakan kungiyar ISIL masu da’awar jihadi kan yi amfani da makamai masu guba akai akai, yayin gumurzun da ake yi na sake kwato birnin Mosul daga hannun kungiyar, kuma sojoji da dama aka jikkata.


Rundunar hadin guiwa dake yakar ‘yan kungiyar ISIL a kasar Iraqi ta sanar cewa mayakan kungiyar ta ISIL sun so su hana dakarun dake yakar su kwace yankin na Mosul inda suka rika amfani da makamai masu guba amma sai ya kasance babu barna sosai.

Rundunar ta ce harin da aka kai masu ranar Asabar babu wanda ya rasa rai amma kuma akwai wadanda aka raunata a kokarin da ake yi na kwace ilahirin birnin daga hannun ‘yan kungiyar ISIL.

Dakarun Iraki dake samun goyon bayan rundunar hadin gwiwa yanzu haka sun yi nasarar kwace ikon gabashin birnin Mosul daga hannun ISIL a yayin da yanzu suka nausa yammancin birnin, Mosul ya kasance gari na biyu mafi girma a Iraki, kuma kungiyar ISIL ta kwashi fiye da shekaru biyu tana iko da yankin.

Watanni shida kenan da rundunar sojin iraki da kawayenta suka kaddamar da farmakin kwato birnin, fararren hula fiye da 300 ne suka rasa rayukansu acewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya.