rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 112 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai kan ayarin motocin safa a Syriya

media
Gawawakin mata da yara warwatse a kasa, bayan kai harin kunar bakin waken da aka kai a Alepo Social Media Website via Reuters TV

A kalla mutane 112 ne suka rasa rayukansu a jiya assabar lokacin da wani dan kunar bakin wake, ya tarwatsa motar da yake ciki a tsakiyar motocin safa dake jigilar kwashe fararen hula a tsohon birnin nan mai tarihi na kasar Syria Alepo, dake rike ga dakarun gwamnatin Bashar a’ Assad, kamar yadda kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar (OSDH) ta sanar.


Kungiyar kare hakkin dan adam din ta ci gaba da cewa « dan kunar bakin waken ya tuka motar skori-kura ne da dauke da kayayyakin agajin abinci, inda ya tarwatsa ta a daura da ayarin motocin safa 75 dake aikin kwashe fararen hula daga Rachidin, ta anguwar yan tawaye a yammacin Alepo inda bayan mutuwa mutane da dama kuma suka jikkata.

A wadannan motocin safa ne dai, a ranar juma’a ar da ta gabata, aka yi nasarar kwashe fararen hula dubu 5000 daga Foua da Kafraya, garuruwa biyu dake rike ga dakarun Syria

Wakilin AFP a yankin Rachidine ya ce, gane wa idonsa gawwakin mutane da dama, daga cikinsu wasu sun kone kurmus, musaman yara da mata da ke cikin motocin dake cikin motocin fafar zazzaune kafin tashin Bam din, a yayinda kuma wasu gawawwakin suka kasance warwatse a gefen motocin na Safa dasuka yi kaca kaca sakamakon karaf fashewar.

Kafin kai wannan hari dai, an kawashe dubban fararen hula da suka makale a garuruwa 4 da dakarun gwamnatin Bashar Al’assad suka yiwa kawanya a ranar juma’ar da ta gabata sakamakon wata rashin jituwa da ta bulla da ta hana ci gaba da aikin kwashe fararen hular.

Ta bakin kungiyar kare hakkin dan adam ta OSDH a Syria, a ranar juma’ar da ta gabata kimanin mutane dubu 7 aka kwashe, dubu 5000 daga cikinsu daga garuruwan dake rike ga hannun yan tawaye ne na Fuwa da Madaya , wasu dubu 2.200kuma daga Zabadani.

Wannan aiki na kwashe fararen hular na karshe da ya dau lokaci mai tsawon ana yi ba tare da haifarmasa tarnaki ba tun bayan barkewar yakin basasar kasar ta Syria, yazo ne bayan cimma wata yarjejeniya tsakanin kasar Qatar, dake goyon bayan yan tawaye, da kuma Iran mai goyon gwamnatin Bachar al-Assad.

Bayan motocin safa sun kwashe fararen hular kauyukan Foua da Kafraya an ga yan tawayen sun doshi birnin Damas da kuma yankin yammacin Lattaki daga birnin na Alepo yankuna masu karfi dake rike ga gwamnatin kasar.

Mutanen da aka kwashe daga Madaya da Zabadani za a kaisu ne a wani yankin yan tawaye na Idleb arewa maso yammacin kasar ta Syria.

to amma sakamakon rashin jituwar da ta bulla ta haifar da datse mutanen da ake kwashewa a unguwanin Fuwa da Kafraya a Rachidine, a yayin da na unguwarnin Madaya da Zabadani ke ci gaba da jira a Ramusa, dake karkashin ikon gwamnati a yammacin birnin na Alepo.

Wani shugaban yan tawaye ya sanar da AFP cewa, an samu sabani ne akan yawan dakarun da za a kwashe ne.

A jimilce dai, sama da mutane dubu 30 000 ne ya dace a ce an kwashe a zanguna 2, kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma a cikin watan maris din da ya gabata tsakanin bangarorin 2 ta tanada.

Tingayen ‘yan tawayen 2 ne, dakarun gwamnatin Syriya suka kwace tare da taimakon kasar Rasha , da ta shiga yakin na Syriya gadangadan tun watan seftamba Shekara ta 2015.