rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi ISIL

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yaki a Mosul ya raba mutane rabin miliyan da gidajensu

media
Rabin Miliyan suka tserewa yaki a Mosul na Iraqi REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya tace watanni shida da aka kwashe ana fafatawa don neman karbe birnin Mosul daga hannun kungiyar mayakan ISIS ya raba mutane kusan rabin miliyan da gidajensu.

 


Lise Grande, jami’ar aikin jinkai na Majalisar a Iraqi ta ce adadin yan gudun hijirar da ke ci gaba da ficewa Mosul na dada karuwa.

Jami’ar ta ce, hasashen da suke da shi na mutanen da ke iya barin garin kafin fara yakin bai wuce miliyan guda ba, amma yanzu haka sama da 493,000 sun fice daga garin, ba tare da daukar komai ba, yayin da adadin ke ci gaba da karuwa.

Majalisar tace yanzu haka akwai mutane 500,000 da rikicin ya ritsa da su a yankin da mayakan ISIS ke rike da shi.

A wata ziyara da ya kai sansanonin mutanen da rikicin Mosul ya raba da gidajensu, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana ayyukan jin kai na bukatar tallafi domin kula da yan gudun hijirar.