rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Hassan Rouhani

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran ta hana Mahmud Ahmadinejad tsayawa takara

media
Tsohon shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad © Reuters

Majalisar kolin malaman Iran, ta haramta wa tsohon shugaban kasar Mahmud Ahmadinejad da ya shugabancin kasar daga 2005-2013, sake tsayawa takara a zaben da za’a yi a watan gobe.


A gefe guda kuma majalisar ta amince da takarar shugaban kasa mai ci, Hassan Rouhani tare da wasu ‘yan takarar guda biyar.

Sauran ‘yan takarar da za su fafata a wannan zabe sun hada ne da Ebrahim Ra’isi, Mustfa Mirsam da kuma Muhd Bagher Qalibaf, dukkansu masu zafin ra’ayi.

A bangaren 'yan takarar masu sassaucin ra'ayi kuma, sun hada ne da Mostafa Hashemitaba, da Eshaq Jahangiri mataimakin shugaban kasar mai ci.

Sama da mutane 1,600 ne suka gabatarwa majalisar malaman karkashin Ayatollah Ali Khamenei bukatunsu na neman tsayawa takarar shugabancin kasar da za’a yi a ranar 19 ga watan Mayun gobe, inda ita kuma majalisar ke tabbatar da mutane 6 kawai.

Sai dai abin lura a nan babu ko da mace daya, da aka tabbatar daga cikin jerin 'yan takarar mata su 130 da suka nemi majalisar ta basu damar tsayawa takarar.

A makon da ya gabata ne a wani mataki na bazata, tsohon shugaban kasar Iran Ahmadinejad mai tsatsauran ra’ayi, ya yanki tikitin tsayawa takara duk da cewa da farko ya ce ba zai sake neman mukamin ba.

Wanda daga karshe a Juma’a nan, majalisar kolin malaman da ke kokarin tabbatar da dorewar juyin juya halin musuluncin kasar ta Iran ta tsame daga cikin jerin 'yan takarar.