Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta yi barazanar nutsar da jirgin yakin Amurka

Kasar Korea ta Arewa ta yi barazanar nutsar da katafaren jirgin ruwan sojin Amurka mai dakon jiragen yaki, dake cigaba da tunkarar yankin na Korea.

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un tare da sauran mukarraban gwamnatinsa yayin duba wasu daga cikin manyan makamai masu linzamin da kasar ta mallaka.
Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un tare da sauran mukarraban gwamnatinsa yayin duba wasu daga cikin manyan makamai masu linzamin da kasar ta mallaka. Reuters/路透社
Talla

Zalika gwamnatin Korea ta arewan ta ce zata kai hari da makamin nukiliya kan kasar Australia muddin ta kuskura ta goyi bayan yunkurin kai mata hari da kasar Amurka ke yi.

Tun a farkon makon da ya gabata shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarnin girke sojin kasar a yankin Korea a matsayin martani kan gwajin makaman da Korea ta Arewan ke shirya cigaba da yi, da kuma barazanar da take na kai wa Amurka hari.

A baya dai kasar China ta yi gargadin cewa, tilas kasashen biyu su kaucewa yaki, kasancewar babu wata kasa tsakanin Korea ta Arewa da Amurka da zata yi nasara a yakin da ke neman barkewa tsakaninsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.