rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Syria Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta sanyawa Mutane 271 takunkumi a Syria

media
Donald Trump shine shugaban Amurka na 45 REUTERS/Kevin Lamarque

Amurka ta sanar da sanya takunkumi kan wasu jami’an gwamnatin Syria 271 saboda abinda ta kira hannun da suke da shi wajen amfani da makami mai guba kan fararen hula.


Baitulmalin Amurka ta bada umurnin rufe daukacin asusun ajiyar jami’an da ke aiki a Cibiyar gudanar da kimiya da Fasaha ta Syria da ke Amurka da kuma hana duk Amurkawa hulda da su.

A ranar 4 ga wannan watan ne aka kai hari da makamin mai guba a Yankin Idlib wanda ya hallaka mutane 87.

Bayan harin Amurka ta kai harin makamai tashar jiragen saman Syria.