Harin Jirgin yakin Amurka ya kashe mayakan al-Qaeda 5 a Yemen
An kashe mambobin kungiyar Al-Qaeda 5 a wani harin da jirgin yakin Amurka ya kai a safiyar lahadi kan wata mota da ke dauke da makamai, a yankin tsakkiyar kasar Yemen.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mahukunta sun bayyana cewa, an harbi motar ne a lardin Al-Jawia cikin yankin Marib da ke gabashin Sanaa, motar da ake kyautata zaton ta shugaban al-qaeda ce ta jigilar makamai.
Ko a ranar 29 ga watan janairun da ya gabata, an fuskanci hare hare ta kasa daga sojojin kasar Amurka a kokarinsu na yakar kungiyoyin jihadi.
Sai dai harin na wannan lokaci ya haifar da mutuwar daya daga cikin dakarun Amurka da fararen hula da dama.
A ranar Assabar wasu mayakan kungiyar Al-qaeda uku sun rasa rayukansu a wani hari makamancin wannan da Amurka ta kai a kudancin kasar ta Yamen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu