Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Shirin gwajin Nukiliyar Koriya ya kankama

Kasar Koriya ta Arewa ta yi gargadin cewar tana iya gudanar da gwajin makamin nukiliyarta a ko wane lokaci, da zarar shugaban kasar ya bayar da umurni.

Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-un, a fadar gwamnatinsa Pyongyang
Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-un, a fadar gwamnatinsa Pyongyang Ed JONES / AFP
Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ya ce kasar a shirye ta ke ta mayar da martanin da ya dace ga kasar Amurka a duk lokacin da ta takale ta.

Jami’in ya ce gwamnatin Koriya za ta ci gaba da shirinta na nukiliya har sai Amurka ta dakatar da duk wata barazanar da ta ke kasar.

Wannan na zuwa a yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta haduwa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un.

A cewar Trump, idan har ya zama wajibi su hadu, to zai so su gana.

Koriya ta Arewa ta gudanar da gwajin makamin nukiliya sau 5 a cikin shekaru 11, matakin da ke razana Amurka da kawayenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.