Isa ga babban shafi
Falasdinu-Isra'ila

Hamas ta gabatar da sabbin manufofi kan Israila

Kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta gabatar da sabbin manufofin ta da suka hada da saukaka matsayin ta kan kasar Isra'ila da kuma amincewa da kasar Falasdinu a kan iyakokin ta na shekarar 1967.

Khaled Mechaal na Kungiyar Hamas
Khaled Mechaal na Kungiyar Hamas KARIM JAAFAR / AFP
Talla

Kungiyar ta kuma ce adawar ta ba da Yahudawa ta ke yi ba saboda addinin su, sai dai tana adawa ne da mamayar da Isra'ila ta yi mata.

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Khaled Meshaal ya shaidawa manema labarai cewar sabon matsayin na su na amincewa da iyakokin shekarar 1967 ba wai amincewa da kasar Isra'ila bane kamar yadda kasahsen duniya ke bukata.

Meshaal ya ce Hamas tana kan matsayin ta na amincewa da Yancin kasar Falasdinu wanda ke dauke da Birnin Kudus a matsayin babban birnin ta da kuam barin 'yan gudun hijirar da suka fice daga Yankin komawa kasar da kuma barin wadanda aka raba da gidajen su komawa gida.

Wannan ba karamar ci gaba bane dangane da matsayin kungiyar ta Hamas wadda kasashen duniya ke kallon ta a matsayin wadda ke zagon kasa ga duk wani yunkurin sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya.

Kuma wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Mahmud Abbas ke shirin tafiya Amurka dan ganawa da shugaba Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.