rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An tafka muhawarar karshe tsakanin 'yan takarar shugabancin Iran

media
'Yan takarar shugabancin Iran guda shida, ciki harda shugaban kasa Hassan Rouhani. ATTA KENARE / AFP

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya kare manufofinsa a yau Juma’a, yayin fafatawarsa da abokan hamayya, a muhawara ta karshe da suka yi, kafin gudanar da zaben shugabancin kasar.


Rouhani dai na fuskantar ‘yan takarar shugabancin kasar guda biyar, a zaben da za’a yi a ranar 19 ga watan da muke ciki.

Kamar yadda suka soki manufofin Rouhani Yayin muhawarori guda biyu da suka gabata, ko a wannan karon ma manyan ‘yan takarar shugabancin kasar ta Iran da suka hada da Ebrahim’ Ra’isi da kuma magajin Birnin Tehran Muhd Baqir Qalibaf, sun bayyana gazawar gwamnatin Rouhani da cewa bata iya tabuka wani abun azo a gani ba wajen inganta jin dadin rauyuwar Iraniyawa duk da dage takun-kuman karya tattalin arziki da kasashen yanmma suka yi.

Zalika ‘yan takarar sun zargi Rouhani, da mika kai ga kasashen yamma ba tare da kare kimar kasar ba.

Shi kuwa a bangarensa Rouhani sukar abokan hamayyarsa tasa yayi da cewa suna daga cikin masu marawa ra'ayin rikau baya, wanda ya haifar da tauye hakkin 'yan kasar a mabanbantan lokuta, ta hanyar amfani da dakarun kare juyin juya halin Jamhuriyyar Musulunci.

Shugaban na Iran ya kuma kare gwamnatinsa da cewa, tana iyaka bakin kokarinta wajen inganta rayuwar al'ummar kasar, tare da jadda cewa Iraniyawa a halin yanzu suna bukatar yanci ne na rayuwa da siyasa ba irin manufofin da abokan hamayya ke kokarin tabbatarwa ba.

Masu sharhi dai na ganin zai wahala shuagban na Iran ya samu kashi 50 na kuri’u da yake bukata a ranar 19 ga watan da muke ciki ta yadda ba sai an sake zagaye na biyu ba kamar yadda ta auku a shekarar 2013 a lokacin da yai lashe zaben shugabancin kasar, saboda hasashen mai yiwuwa a samu nokewar wasu da suka jefa masa kuri’a a baya.

Hakan kuwa na da nasaba da yadda Jagoran Addini a Iran din Ayatolla Al Khomeini ke sukar yadda dage takun-kuman da aka kakabawa Iran ya gaza yin tasiri wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar.