Isa ga babban shafi
Amurka

Dole mu kawo karshen barazanar Korea ta Arewa - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci majalisar dinkin duniya ta kakabawa kasar Korea ta Arewa Karin takunkumin karya tattalin arziki, bayan gwajin makami mai linzamin da ta yi yau Lahadi.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Trump da ya bayyana sabon gwajin a matsayin tsokana, wadda ya ce kamata yayi ya zama hujjar sake kakabawa Korea ta Arewan takunumi ba tare da bata lokaci ba.

Hukumomin tsaron kasar Japan sun ce makamin yayi tafiyar sama da kilomita 700 kafin ya fada tekun Japan, nisan kilomita 500 daga kan iyakar kasar Rasha.

Jerin takunkuman da a baya aka kakabawa Korea ta Arewa karkashin jagorancin Amurka da majalisar dinkin duniya, ya gaza yin tasiri wajen dakatar da kokarinta na kera makaman nukiliya da gwajin makamai masu linzami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.