Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta sake gwajin makamai masu linzami

Kasar Korea ta Arewa, ta sake gudanar da gwajin makamai masu linzami, kwanaki kadan bayanda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa a shirye yake, ya tattauna da shugaban kasar Korea ta Arewan, Kim Jong-Un, don kawo karshen tsamin dangantakar kasashen biyu.

Manyan makamai masu linzami na kasar Korea ta Arewa yayinda ake wucewa da su ta gaban shugaban kasar Kim Jong Un da wasu manyan mukarrabansa a babban birnin kasar Pongyang.
Manyan makamai masu linzami na kasar Korea ta Arewa yayinda ake wucewa da su ta gaban shugaban kasar Kim Jong Un da wasu manyan mukarrabansa a babban birnin kasar Pongyang. Reuters/路透社
Talla

Nisan makamai masu linzamin da kasar Korea ta Arewan ta gwada dai ya kai kilomita dubu biyu (2,000) zuwa sararin samaniya, kamar yadda jami’ai a kasar Japan suka tabbatar.

Sabon shugaban kasar Korea ta Kudu, Moon Jae-in, da a baya ya sha alwashin kyautata dangantakar diflomasiyya da Korea ta Arewa, ya bayyana gwajin makaman a matsayin tsokanar da aka shirya ta da gangan.

Jerin gwaje gwajen makamai masu linzamin da Majalisar Dinkin Duniya ta haramta, wadanda kasar Korea ta Arewa ta yi cikin wannan shekara, ya haddasa zaman dar dar, musamman a wasu kasashen turai, tare da dada kamarin tsamin dangantakar da ke tsakanin Korea ta Arewan da kasar Amurka, da ke barazanar yin amfani da karfin soji a kanta, don kawo karshen gwajin makaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.