rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Hukumar kasuwanci ta duniya China Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taron farfado da hanyoyin kasuwanci a Duniya a China

media
Taron farfado da hanyoyin kasuwanci a Duniya a China REUTERS/Wang Zhao/Pool

Kasar China na ci gaba da sabon yabo saboda yunkurin da tayi na bunkasa harkokin kasuwancin ta a duniya.
Akalla shugabanin kasashe 30 ke halartar taron kwanaki biyu da ake gudanar a Beijing kan farfado da hanyoyin kasuwanci da akayi tsakanin Asia da Turai da Afirka, kuma cikin mahalarta taron harda shugaban Rasha Vladimir Putin da na Turkiya Recep Tayyip Erdogan.
 


Shugaba Xi Jinping a wajen bude taron ya yi tayin zuba Dala biliyan 124 wajen inganta tashoshin jiragen ruwa da na kasa da hanyoyin motoci.
Sakataren kudin Birtaniya Philip Hammond ya ce a shirye suke suyi aiki tare.
Ana sa ran Shugabanin kasashe dake halartar wannan taro na China za su samar da hanyoyin ceto tattalin arziki da ma bunkasa kasuwanci a kasashen ma su tasowa.