Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta sake tsokanar fada

Kasar Korea ta Arewa, ta sake yin gwajin wani makami mai linzami, duk da barazanar sake kakabata takunkumin karya tattalin arziki da Amurka ke yi.

Kumbon daukar makami mai linzami da ke shafe dogon zango, wanda kasar Korea ta Arewan ta yi gwajin harba shi a baya-bayannan.
Kumbon daukar makami mai linzami da ke shafe dogon zango, wanda kasar Korea ta Arewan ta yi gwajin harba shi a baya-bayannan. Reuters/路透社
Talla

Karo na biyu kenan, Korea ta Arewan ke gwajin makamin cikin mako guda, kuma karo na 8 a cikin wannan shekarar.

Jerin gwajin makaman da korea ta Arewan ke yi, yana cigaba da jawo ala-wadai daga kasashen duniya musamman na turai, saboda abinda suka kira sabawa dokar Majalisar Dinkin Duniya kan irin gwajin da ta haramta.

A sanarwar data fitar jiya asabar, gwamnatin Kim Jong-Un ta ce barazanar da ake mata, na kakaba mata sabbin takun-kuman karya tattalin arziki ba zai hanata inganta karfin mallakar makaman nukiliya domin kare kanta daga barazanar kasashe kamar su Amurka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.