Isa ga babban shafi
Syria

Mayu ya zama wata mafi muni ga 'yan kasar Syria

Hare-haren da dakarun Amurka suka kai a Syria, sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 225 a cikin wata daya.

Wasu fararen hula da ake kwashewa daga yankunan Syria da ke hannun 'yan tawaye.
Wasu fararen hula da ake kwashewa daga yankunan Syria da ke hannun 'yan tawaye. REUTERS/Ammar Abdullah
Talla

Adadin mafi yawa da aka samu a cikin wata daya tun daga shekara ta 2014.

Kungiyar da ke sa-ido kan lamurran da ke faruwa a Syria ta ce daga 23 ga watan Afrili zuwa 23 ga wannan wata na Mayu, aka yi wannan kisa, cikin har da kananan yara 44 dakuma mata 36 wadanda sojin Amurka suka kashe.

Zuwa yanzu jimillar wadanda suka rasa rayukansu sakamakon yakin da kasar Syria ta tsinci kanta ya kai fararen hula, 1, 481, daga ciki kananan yara akalla 319.

A ranar 23 ga watan Satumban shekara ta 2014 Amurka ta kaddamar da hari kan mayakan IS a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.