Isa ga babban shafi
Myanmar

Facebook ya toshe shafuka a Myanmar saboda Musulunci

Facebook ya toshe shafukan mutane da dama a Myanmar akan wata kalma ta nuna kyama ga musulmi da ya haramta amfani da ita a shafukan mutanen kasar. Matakin dai ya janyo cece-kuce musamman kan yadda Facebook din ya toshe har shafukan masu adawa da rubuta Kalmar ta “Kalar” da ke nufin bakin haure.

Kamfanin Facebook ya toshe shafukan mutane a Myanmar saboda kyamar Musulmi
Kamfanin Facebook ya toshe shafukan mutane a Myanmar saboda kyamar Musulmi REUTERS/Regis Duvignau/File Photo
Talla

Kalmar ta Kalar na nufin Bakin haure, kalmar da mutanen kasar ta Myanmar ke dangantawa da musulmin kasar.

Yanzu haka dai matakin toshe shafukan na Facebook ya janyo cece-kuce yayin da wasu suka fara kiran gudanar da gagarumar zanga-zanga a ranar Laraba.

Facebook dai na fuskantar kalubale na dakile kalaman batanci ga wani ko addini ko wata kabila.

Wasu daga cikin mutanen na Myanmar sun bayyana damuwa kan yadda Facebook ya toshe shafinsu duk da cewa sun rubuta kalmar ta Kalar akasin kyamar Musulmi.

Amma kamfanin Facebook ya fito ya bayyana cewa wani lokaci yana kuskure a kokarin da ya ke na tsabtace shafin.

Gwamnatin Myanmar dai ta ce, ba da yawunta Facebook ya dauki matakin ba.

Yanzu dai mutane kusan 2000 su ka shirya yin zanga-zanga a Yangon domin adawa da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.