wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 27 a Iraqi

Hukumomin tsaron Iraqi sun bayyana cewa, wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane 27 bayan ya tayar da bama-baman da ke makare a cikin motarsa a wani shagon cimaka a birnin Bagadaza.
Harin wanda aka kai a dai dai lokacin da jama’a ke bude bakin azumin Ramadan, ya kuma raunana mutane 30.
Kafar Amaq da kungiyar ISIS ke yada farfagantarta, ta rawaito cewa, an kai harin ne kan mabiya Shi’a a kasar.
Kungiyar ISIS dai na kallon mabiya Shi’a a matsayin ‘yan bidi’a , abin da ya sa ta ke yawan kaddamar mu su da hare-hare a kasar.