Isa ga babban shafi
Yemen

Duniya ta yi burus da yakin kasar Yemen-O’Brien

Majalisar Dinkin Duniya ta sake daga muryar ta kan abinda ta kira yadda kasashen duniya suka nade hannun su suna kallon kasar Yemen na ci gaba da rugujewa.

Shugaban hukumar aikin jinkai na MDD Stephen O'Brien
Shugaban hukumar aikin jinkai na MDD Stephen O'Brien AFP PHOTO / KHALIL MAZRAAWI
Talla

Yakin kasar dai a cewar Majalisar na ci gaba da daidaita mutanen ta da ke fama da yunwa da kuma annobar kwalara.

Shugaban hukumar aikin jinkai na Majalisar Stephen O’Brien ya shaidawa kwamitin Sulhu cewar babu wani lokacin da ya dace na magance matsalar yunwan kasar da kuma sanya ta kan tafarkin tsira daga matsalolin da suka addabe ta.

Jami’in ya ce abin takaici ne yadda talakawan Yemen ke dandana azabar tashin hankali da yunwa da cutar kwalara wadda ke ci gaba ad hallaka jama’a, yayin da kasashen duniya suka yi ko oho.

Mutane sama da 8,000 aka kashe tun bayan kaddamar da yakin da Saudi Arabia ta yi a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.