rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Taliban Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Harin Kabul ya kashe mutane sama da 80

media
Ofisoshin jekadancin kasashe da dama sun kone a harin Kabul REUTERS/Omar Sobhani

Wani Kazamin harin bam da aka kai a unguwar da ke dauke da ofisoshin diflomasiya a birnin Kabul kasar Afghanistan ya hallaka mutane sama da 80 tare da jikkata daruruwa. Harin ya lalata Ofisoshin jekadancin kasashe da dama a Kabul wanda aka kai a wannan wata mai alfarma na Ramadan.


Ma’aikatar lafiya ta Afghsnitan ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon harin sun kai mutane 80 sannan sama da 300 suka jikkata yawancinsu mata da yara kanana.

Sannan hukumomin lafiyar sun ce adadin na iya karuwa a yayin da ake ci gaba da aikin tsamo gawarwakin mutane daga guraguttsan gine-ginen da harin ya tarwatsa.

Harin wanda aka kai da wata motar daukar kaya, ya lalata ofishojin jekadancin kasashe da dama da suka hada da na Faransa da Indiya da Turkiya da Japan da Daular Larabawa.

Mutanen Kabul dai sun ce da farko sun zata girgizar kasa ce saboda yadda suka ji karar fashewar bom din.

Akwai direban Kafar yada labaran Birtaniya ta BBC da harin ya rusa da shi, da ‘yan jarida 4 da suka jikkata.

Babu dai wata kungiya da ta fito da dauki alhakin kai harin, wanda ya tabbatar da girman matsalar tsaro a Afghanistan bayan ficewar dakarun Amurka.