rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

India Dabbobi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta dakatar da dokar hana sayarwa da yanka shanu a India

media
Mabiya addinin Hindu na daraja Shanu AFP PHOTO / Noah SEELAM

Wata Kotu a kasar India ta dakatar da aiwatar da dokar hana sayar da shanu da kuma yankawa da gwamnatin Firaminista Narendra Modi ta amince, abinda ake ganin zai dakile aiki da ita.


A makon jiya gwamnatin ta haram ta saye ko sayar da shanu da niyyar yankawa, saboda yadda mabiya addinin Hindu ke kallon sa da matukar girmamawa.

Umurnin dai ya haifar da zanga zanga ga wadanda basa bin addinin Hindu da suke ganin cewar Jam’iyyar Modi ta Bharatiya Janata na neman tilasta musu bin addinin su.

Wasu Jihohin da suka halarta yanka shanun sun ce dama sub a za suyi amfani da umurnin Firaministan ba.