Isa ga babban shafi
Afghanistan

Ana sukar gwamnatin Afghanistan akan harin Kabul

Wasu mutanen Afghanistan sun dora alhakin mummunan harin da aka kai a Kabul akan gwamnatin kasar, bayan mutuwar mutane 90 yawancinsu fararen hula. Har zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin da aka kai unguwar da mafi yawanci ofishohin jekadancin kasashen waje ne a Kabul.

Harin da aka kai Kabul ya lalata ofisoshin jekadancin kasashen waje da dama.
Harin da aka kai Kabul ya lalata ofisoshin jekadancin kasashen waje da dama. REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Mutanen na ganin akwai sakaci daga bangaren jami’an tsaro, inda suka bukaci gwamnatin kasar ta fito ta yi bayani kan abin da suke ganin akwai gazawa daga bangaren hukumomin leken asiri.

A yau Alhamis dangi sun binne ‘yan uwansu da suka mutu a mummnan harin da aka kai da ya raunana sama da 400.

Wasu mutanen Afghanistan sun bukaci gwamnati ta fito ta yi bayani akan gazawar bangaren hukumomin leken asiri, wadanda za su iya dakile faruwar harin.

Wasu ‘yan kasar na dora laifin harin akan gwamnati domin hakkinta ne na kare rayukan jama’a musamman a bababn birnin kasar.

Hukumar leken asirin Afghanistan ta yi zargi cewa kungiyar Haqqani mai alaka da Taliban ce ta kai harin, yayin da Taliban kuma ta nisanta kanta da harin.

Harin da aka kai jiya a Kabul dai shi ne mafi muni da aka taba kai wa a Afghanistan tun kaddamar da yaki akan Taliban a 2001.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.