Isa ga babban shafi
Turkiya- Amurka

Turkiya ta gargadi Amurka kan taimakawa Kurdawan Syria

Turkiya ta yi gargadin cewar yana da matukar hadari yadda Amurka ke bai wa Kurdawan Syria makamai domin yaki da mayakan ISIS.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Alexander Zemlianichenko
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Mevlut Cavusoglu ya ce matakin kuskure ne domin yana da hadari ga ci gaba da zaman Syria kasa guda.

Ita ma Majalisar tsaron Turkiya ta bayyana cewar bai wa Kurdawan makamai ya sabawa yarjejeniyar kawancen da kasashen suka shiga.

Shugaba Donald Trump ya bada umurnin bai wa Kurdawan makamai domin yakar ISIS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.