rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Philippines Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 37 sun mutu a harin da wani ya kai a gidan caca

media
Hari a gidan cacar kasar Philippines REUTERS/Erik De Castro

‘Yan sanda a Philippines sun tabbatar da gano gawarwakin mutane 36 a wani gidan caca da ya kone kurmus sakamakon harin da wani dan bindiga ya kai wata otel a Manila.Bayanai dai sun nuna cewa wani mutum ne da ya yi shigar burtu ya kai hari tare da kona gidan cacar.


Dan bindigar ya kai harin ne da asuba yau Juma’a inda ya abka wani daki da ake caca cikin wata otel a Manila ya bude wuta da bindiga kirar M4 tare da kashe kansa ta hanyar cinnawa kansa wuta da Fetir.

‘Yan sanda manila sun ce hayakin da ya turmuke dakin cacar ne ya yi sanadin mutuwar mutane 37.

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan dan bindigar musamman asalinsa. Amma kungiyar IS ta fito ta yi ikirarin cewa daya daga cikin mayakanta ne ya kai harin.

Amma hukumomin Manila ba su danganta harin da na ta’addanci ba. ‘Yan sandan Philippine sun ce suna tunanin dan bindigar ya je yin fashi ne saboda yadda bai harbi kowa ba a dakin cacar, illa wajen da aka ajiye kudi.