Isa ga babban shafi
Iran

Khamenei ya soki alakar Saudiya da Trump

Shugaban Addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya caccaki kawancen da Amurka da Saudi Arabia suka kulla don yaki da kasarsa, yana mai cewa shirin ba zai haifar da "Da mai ido ba".

Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei
Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei HO / IRANIAN SUPREME LEADER'S WEBSITE / AFP
Talla

A jawabin da ya yi wa al’ummar Iran ta kafar talabijin, Khamenei ya ce duk da cin hancin da Saudiya ta bai wa Amurka na kwangilar dala biliyan 110, kasar ba za ta cimma burinta a Yankin Gabas ta Tsakiya ba.

Shugaban ya zargi Amurka da harshen damo, wajen kauda kanta kan irin kisan gillar da Saudiya ke yi a Yemen, yayin da a bangare guda ta ke ikirarin kare hakkin Bil Adama a duniya.

A cewar Khamenei, hare haren da kungiyar IS ke kai wa a kasashen Turai ya nuna akwai bukatar kasashen na yammaci su koma su yi nazari ga huldarsu a kasashen gabas tsakiya.

A ziyarar da ya kai Saudiya, shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Iran a matsayin babbar kasar da ke tallafawa ‘yan ta’adda.

Yarjejeniyar Nukiliya da Iran ta kulla tsakaninta da manyan kasashen duniya ya taimakawa wajen daidaita hulda tsakanin Tehran da Wahington.

Amma ana ganin Trump na iya yin watsi da yarjejeniyar, kamar yadda ya sha sukar yarjejeniyar a yakin neman zabensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.