Isa ga babban shafi
Myanmar

Jirgin saman Myanmar ya bace dauke da mutane 116

Wani Jirgin Sojan Myanmar ya bace dauke da mutane 116 yawancinsu Sojoji da iyalansu. Rahotanni sun ce an ga wasu tarkacen jirgin a tekun Andaman da ake tunanin ya fadi a yau Laraba.

REUTERS
Talla

Jiragen ruwa da na sama na ci gaba da aikin binciken jirgin wanda ba a sake jin duriyarsa ba bayan katsewar sadarwa tsakaninsa da masu kula jiragen sama.

Akwai yara da dama da ke cikin jirgin wanda ya taso daga Myeik zuwa Yangon.

Jirgin na dauke da mutane 116 yawancinsu sojojin kasar da iyalansu.

Rundunar sojin Myammar ta ce an samu katsewar sadarwar jirgin da misalin karfe 1:30 na rana agogon kasar kuma daga lokacin ba a sake jin duriyar jirgin ba.

Daga lokacin ne jiragen ruwa da na sama suka shiga aikin lalaben jirgin a tekun Andaman da ake tunanin anan ya bata.

Wasu rahotanni sun ce an ga wasu tarkace kamar na jirgin a tekun Andaman.

Ana hasashen tangardar na’ura ce ta haifar da matsala ga jirgin wanda sabo ne da Myanmar ta sayo a watan Maris din bara.

An bayyana cewa duka duka sa’o’I 809 jirgin ya yi a sama tun sayo shi daga China.

Myanmar ta dade tana fuskantar matsala a jiragen sojinta, domin ko watan Fabrairun bara wani jirgin sojan kasar ya kama da wuta jin kadan bayan ya cira sama a tashar babban birnin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.