rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun kai hari a hubbaren Khomeini na Iran

media
Hubbaren Ayatollah Ruhollah Khomeini a birnin Tehran REUTERS

Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi a Majalisar Dokokin Iran da kuma hubbaren jagoran juyin-juya halin kasar Ayatollah Khomeini a birnin Tehran, in da suka kashe akalla mutane 7.


Kafofin yada labaran kasar sun tabbatar cewa, harbe-harben sun jikkata mutane da dama a Majalisar Dokokin yayin da kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai farmakin na yau duk da dai ba ta bada gabatar da wata hujja ba.

Kamfanin Dillancin Labaran IRIB ya rawaito cewa, ‘yan bindigan sun kuma bude wuta kan bakin da ke ziyara a kabarin Khomeini da ke kudancin Tehran, yayin da wani maharin daban ya tayar da bam din da ke jikinsa a hubbaren.

IRIB ya rawaito wani dan Majalisa, Elyas Hazrati da ke bada tabbacin cewa, maharan sun yi amfani da bindigogi kirar AK-47 wajen kai farmakin a Majalisar.

Rahotanni na cewa, akwai alamar cewa an shirya tsaf don kai wa kasar hari a wannan Laraba, lura da cewa an kai hare-haren ne lokaci guda a Majalisar Dokoki da kuma kabarin Ayatollah Khomeini.