rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tarayyar Turai ta karfafa takunkumi akan Koriya ta Arewa

media
Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamai sau 12 REUTERS

Kungiyar Tarayyar Turai ta kara zafafa takunkumin da ta malkayawa kasar Koriya ta arewa saboda ayyukan Nukiliya da gwaje gwajenta na makamai masu linzami


Kungiyar ta fadi cewa za ta rufe asusu da kadarori na wasu mutane akalla 14 da hana su tsoma kafarsu a Turai kamar yadda Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a yi makon jiya, kan karfafa wa Koriya takunkumi kan gwajin makaman da kasar ke yi masu hadari.

Kungiyar Tarayyar Turai ta kuma malkaya wa wasu kamfanonin Koriya takunkumi.

Zuwa yanzu mutane 94 ‘yan kasar Koriya ta Arewa takunkumin Tarayyar Turai ya shafa, da kamfanoni 53.