rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Qatar Saudiya Masar Bahrain

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiyya ta fitar da sunayen 'yan ta'adda da ta ce Qatar na mara wa

media
Ministan harkokin wajen Qatar, Mohammed ben Abderrahman al-Thani. KARIM JAAFAR / AFP

Qatar ta yi watsi da hujjojin da Saudiyya da kawayenta suka bayar da ke bayyana jerin sunayen ‘yan ta’adda da suka ce kasar na mara wa baya a sassan duniya.


Sanarwar hadin-gwiwa ta kasahen Saudiyya, Bahrain, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, ta bayyana jerin wasu daga cikin kungiyoyin da ake zargin cewa Qatar ce ke taimaka ma su.

To sai dai gwamnatin ta Qatar ta fitar da sanarwa da ke watsi da wannan zargi. Yanzu haka dai kasashen na Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya, sun katse duk wata huldar diflomasiyya, ta sufuri, kasuwanci da dai sauransu da wannan karamar kasa da ke yankin tekun Fasha.