rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Turkiya Qatar Saudiya Bahrain

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cavusoglu ya kare manufar girke sojin Turkiya a Qatar

media
Ministan harkokin waje na Turkiya, Mevlut Cavusoglu REUTERS/Vincent Kessler

Ministan harkokin wajen kasar Turkiya, Mevlut Cavusoglu, ya ce, manufar kafa katafariyar cibiyar sojin kasar, da zata fara aiki gadan gadan a kasar Qatar, ita ce tabbatar da tsaron baki dayan yankin tekun Fasaha ko kuma Gulf.


Cavusoglu ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da yayi da takwaransa, a birnin Isatanbul, wato ministan harkokin waje na kasar Bahrain, Shiekh Khalid bin Ahmed, inda ya ce Turkiya zata cigaba da kokarin sasanta, tsakanin Qatar da sauran kasashen Larabawa da suka yanke hulda da ita, cikin harda kasar ta Baharain, bisa zargin goyawa ta’addanci baya.

A ranar Larabar da ta gabata, majalisar Turkiya ta amince da kudurorin, girke sojin kasar a Qatar, tare da fara horar da jami’an sojinta.

A watan Afrilun shekara ta 2016, Turkiya da Qatar suka sanya hannu kan kulla yarjejeniyar inganta alakar sojinsu, a birnin Doha.