rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Qatar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran ta aikawa Qatar da kayan abinci

media
Yanke hulda da kasashen Larabawa suka yi da Qatar ya yi tasiri ga kasar REUTERS/Naseem Zeitoon

Kasar Iran ta aike da manyan jiragen sama biyar cike makil da kayayyaki marmari na abinci zuwa Qatar, kwanaki bayan manyan kasashen Larabawa sun yanke hulda da ita, wanda ya yi tasiri ga harkokin sufuri da kasuwanci a tsakaninsu.


Jiragen na dauke ne da ton 90 na kayan marmari da na lambu da aka fi bukata a wanann lokaci na azumin Ramadan.

Kakakin ma’aikatar sufurin jiragen Iran Shahrokh Noushabadi ya ce za su ci gaba da kai wa Qatar daukin kayan abinci muddin akwai bukatar haka.

Kamfanin dillacin larabaran Iran na Tasnim ya ruwaito cewa akwai jiragen ruwa 3 da aka cika makil da ton 350 na kayan abinci da ke kan hanyar isa gabar Qatar ta hanyar tashar ruwan Dayyer da ke kusa da Iran.

Iran ta kuma bude hanyar jiragen samanta ga jirage 100 da za su yi hada-hada da Qatar, bayan Saudiya da Bahrain da Daular larabawa sun haramtawa jiragen kasar amfani da sararin samaniyarsu.

Matakin Iran a yanzu ya habbaka hada-hada a Qatar da kashi 17 cikin 100.

Iran ta yi kira ga Qatar da sauran kasashen Larabawa su rungumi tattaunawar sasantawa domin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.