rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Annobar Kwalara ta kashe mutane 923 a Yemen

media
Kwalara na ci gaba da yaduwa a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah

Majalisar Dinkin Duniya ta ce annobar kwalara na sake yaduwa a kasar Yemen inda a kowani minti guda ake samun wanda ake kwantarwa a Asibiti. Alkallumar Majalisar na cewa yanzu mutane dubu 124 ke dauke da cutar, bayan 923 da suka kwanta dama.


Majalisar ta ce Asibitin Al-Sabiine da sauran asibitoci kasar sun cika makil da daruruwan mutane da ke fama da matsanancin Kwalara, abin da ya tilasta kafa musu rumfuna a waje da kan tittuna.

Yakin da ake fama da shi a kasar ya haifar da rashin tsafta da gaza bai wa masu fama da wannan annoba dauki kamar yadda ake bukata.

A cewar jami’an kiwon lafiyan kasar, a cikin makonni biyu da suka gabata, a kullum sai an samu mutum daya, ko biyu ko Uku da ke kamuwa da cutar a kasa da minti guda.

Dakta Ismail Mansouri wani likita ne da ke shaida muni da kwalara ya yi a kasar, ya ce cibiyar Mahel al-hada da ke hana yaduwar kwalara a kasar, na karban mutane 300 a kullum, ga rashin magugguna da ake fama da shi.

Likitan ya shaida cewa hare-hare da aka kai cikin watan Mayun da ya gabata a inda aka tara shara, ya sake ta’azara annobar.

Annobar da ta bula tun 27 ga watan Afrilu a kasar da yaki ya tagayara, na yaduwa kamar wutan daji a sassan kasar, dalilan da ya sanya Majalisar Dinkin Duniya gargadi don shawo kan ciwon tun kafin saukar ruwan sama mai karfi, ga kuma yanayi na yunwa da rashin abinci mai gina jiki.