rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Hamas Falasdinawa Gaza

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Hamas ta cika shekaru 10 a Gaza

media
A ranar 15 ga watan Yunin 2007 ta karbi ragamar shugabanci a Gaza bayan gwabza fada da Fatah REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa

Kungiyar Hamas ta cika shekaru 10 da karbe mulki a yankin zirin Gaza, yankin da ke fama da barazanar rikici da rashin wutar lantarki da talauci da kuma takunkumin Isra’ila.


An kafa kungiyar Hamas a ranar 14 ga Disemban 1987, bayan rikicin Falasdinawa na farko da ake dangantawa da Intifada.

Kungiyar Hamas na bikin cika shekarun 10 ne a dai dai lokacin da ake fargabar rikicin Gaza zai tsananta saboda barakar diflomasiyar tsakanin kasashen Larabawa da Qatar.

Qatar ta kasance babbar mai bai wa zirin Gaza tallafi amma ana ganin za a tirsasa ma ta rage yawan tallafin da ta ke bai wa yankin.

Matsalar rarrabuwar kai na ci gaba da kamari tsakanin kungiyar Hamas da Fatah ta shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas.

Tun a ranar 15 ga watan Yunin shekarar 2007 ne, kungiyar Hamas ke mulkin Gaza bayan ta karbe daga hannun Fatah a wani rikici da ya kusan zama yakin basasa, kuma bangarorin biyu sun samu barakar ce bayan zaben ‘yan Majalisu da Hamas ta lashe a shekara 2006.

Hamas da sauran kungiyoyin ‘yan tawayen Falasdinawa a Gaza sun gwabza yake-yake har sau uku da Isra’ila.

Fiye da shekaru 10 ke nan da Isra’ila ta kange zirin na Gaza, lamarin da ya jefa tattalin arzikin yankin cikin mawuyacin hali.