rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Pakistan ISIL

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kai harin bam a masallacin 'yan Shi'a a Kabul

media
Wani hari a birni Kabul, Afghanistan cikin watan mayun 2017. REUTERS/Omar Sobhani

Wasu ‘yan kunar bakin wake sun tada bam a wani Masallachin mabiya mazhabar Shi’a da ke Kabul na kasar Afghanistan, inda suka kashe mutane 4 suka kuma jikkata wasu da dama.


Najib Danish, mai magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar, ya ce an kai harin ne a Masallachin Al Zahra da ke yammacin birnin na Kabul.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin, wanda shi ne irinsa na farko da aka kai wa masallacin da mabiya mazhabar ta Shi’a ke ibada cikinsa a wannan wata na Ramadan.