rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi Majalisar Dinkin Duniya Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yawan fararen hula da IS ke garkuwa da su Mosul ya karu

media
Fararen hular da yakin Mosul ya raba da gidajensu. KARIM SAHIB / AFP

Majalisar dinkin duniya, ta ce yawan fararen hular da mayakan IS ke garkuwa da su a birnin Mosul na Iraqi, ya karu zuwa dubu 150 daga dubu 100 da ta sanar a baya.


Shugabar sashin bada agajin gaggawa ta Majalisar a yankin, Lise Grande, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, mayakan na IS suna bude wuta kan duk wani farar hula da yayi yunkurin tserewa daga birnin.

Grande ta ce akalla mutane 7,000 ne aka samu da raunukan harbi a gadon baya, wadanda suka samu, sakamakon yunkrin teserewa daga yankunan da ke karkashin IS da suka yi.

A halin yanzu yawan fararen hular da majalisar dinkin duniya ta yi hasashen zasu tsere daga Mosul ya kai dubu 860, daga dubu 750 da tayi hasashen zasu tsere a baya, sakamakon gwabza yaki da ake tsakanin mayakan IS da sojin Iraqi da kokarin murkushe su tun a watan Oktoban bara.