IS ta rusa masallacin da Baghadi ya kira kansa Kalifa
Magoya bayan kungiyar IS sun tarwatsa masallacin Al-Nuri da shugabansu Abubakar Al-Baghdadi ya gabatar da hudubarsa ta farko a matsayin Khalifa shekaru biyu da suka gabata a birnin Mosul.
Wallafawa ranar:
Laftanal Janar Abdul-Amir Yarallha babban kwamandan rundunar da ke kokarin kwace birnin Mosul, ya ce mayakan na Daesh sun tarwatsa masallacin ne a daidai lokacin da dakarun gwamnati suka doshi masallacin.
Masallacin na daga cikin masallatai mafi dadewa a birnin Mosul mai tarihi a cikin Iraqi.
Gwamnatin Iraqi ta danganta rusa masallacin a matsayin nasara akan Mayakan IS da aka shafe watanni takwas ana yakarsu domin kwato garin Mosul.
A watan Yunin 2014 ne IS ta ayyana kafa daula bayan kwace Mosul, kuma a lokacin ne aka nuna shugaban kungiyar Baghdadi a Masallacin yana huduba tare da bayyana kansa a matsayin Kalifa.
Sai dai kungiyar IS ta ce dakarun Iraqi ne suka rusa masallacin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu