Isa ga babban shafi
Iraqi

Dakarun Iraqi sun yi ikirarin murkushe IS a Mosul

Rundunar Sojin Iraqi ta ce nan da ‘yan kwanaki kadan ne za ta sanar da samun nasarar murkushe IS a Mosul bayan shafe watanni takwas suna gwabza domin kwato birnin.

Wasu Sojojin Iraqi rike da tutar Mayakan IS a Mosul
Wasu Sojojin Iraqi rike da tutar Mayakan IS a Mosul Reuters
Talla

Babban kwamandan rundunar sojin kasar Janar Abdulghani Al Assadi ya ce nan da ‘yan kwanaki za su tabbatar wa duniya da cewa sun gama da IS.

Gwamnatin Iraqi ta ce karbe ikon Masallacin al-Nuri ya tabbatar da samun nasara akan IS.

A ranar 17 ga Oktoba dakarun Iraqi suka kaddamar da yaki domin kwato garin Mosul daga IS.

Kwamandan Sojin na Iraqi ya kiyasta cewa mayakan IS 200 suka rage yanzu a Mosul kuma yawancinsu ‘yan kasashen waje ne.

Gwamnatin Iraqi ta ce babban nasara ce, samun kwace masallacin al-Nuri, daya daga cikin masallatai mafi dadewa a birnin na mosul mai tarihi a cikin kasar ta Iraki.

Masallacin dai ya kwashe shekaru 850 da ginawa, kuma a nan ne shugabansu mayakan IS, Abubakar Al Baghdadi ya gabatar da hudubarsa ta farko a matsayin Khalifa shekaru uku da suka gabata.

An dai kashe fararen hula da dama a fadan da dakarun Iraqi suka kaddamar akan IS a Mosul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.