Isa ga babban shafi
Qatar

Saudiya ta tsawaita wa’adin da ta ba Qatar

Kasashen Larabawa a karkashin jagorancin Saudiya sun tsawaita wa’adin da suka bai wa Qatar na ta cika wasu sharudda guda 13 kafin su janye takunkuman da suka kakakaba wa kasar.

Ministan waje na kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani
Ministan waje na kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani Reuters
Talla

Karin kwanaki biyu ne kasashen suka kara wa Qatar, matakin da Kuweit da ke shiga tsakani game da takaddamar ta bukaci a yi.

Sharuddan 13 sun kunshi har da rufe tashar talabijin ta Aljazeera, da rufe wani barikin sojin Turkiya da ke cikin Qatar, sannan kuma da katse hulda da kasar Iran.

Sai dai ministan harkokin wajen Qatar Mohammed ben Abderrahmane Al-Thani, ya ce ba su da niyyar mutunta sharuddan.

“Duk wani abu da za a yi, ya kamata ya kasance a cikin tsari da kuma bin ka’ida, Wadannan sharudda da aka gindaya mana, lalle ba za mu iya yin hakan ba” a cewar Al Thani.

A ranar Laraba ne ministocin harakokin wajen Saudiya da Daular Larabawa da Bahrain za su hadu a Masar domin tattaunawa kan Qatar.

Amma Ministan harakokin wajen Qatar ya ce ba za su yadda da wasu sharudda ba ko kuma shiga tattaunawa da wata kasa ba, a cewarsa ko za su hau teburin tattaunawa sai idan an shirya ta a cikin kyakkyawan yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.