Isa ga babban shafi
Amurka

Sufuri: Amurka ta dagewa kamfanonin Kuwait da Jordan takunkumi

Gwamnatin Amurka cire kamfanonin sufurin jiragen sama na Kuwait Airways da kuma Royal Jordanian, daga cikin jerin wadanda ta kakabawa haramcin bai wa fasinjojinsu damar daukar na`urorin kamfuta na tafi da gidanka wato laptop zuwa cikin kasar ta Amurka.

Amurka ta dagewa kamfanonin sufurin jiragen sama na Kuwait Airways da kuma Royal Jordanian haramcin daukar na'urorin Laptop
Amurka ta dagewa kamfanonin sufurin jiragen sama na Kuwait Airways da kuma Royal Jordanian haramcin daukar na'urorin Laptop
Talla

Kamfanonin jiragen saman sun ce, an cimma wannan matsayar ce, bayan da suka yi aiki tukuru da jami:an tsaron Amurka, wajen tsaurara matakan bincikar fasinjoji a filayen jiragen saman kasashensu na Kuwaiti da Jordan.

A watan Maris din da ya gabata ne, Amurka ta haramtawa jiragen sama daukar na`urorin Laptop, wadanda ke tasowa zuwa kasar daga wasu kasashen Musulmi guda takwas, bisa fargabar cewa, :yan ta`adda zasu iya amfani da wannan dama wajen boye bama-bamai a na`urorin.

A ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata gwamnatin Amurka, ta sanar da sabbin matakan tsaurara tsaro, wanda ke bukatar karin lokaci wajen bincikar fasinjojin jiragen sama da ke bukatar shiga kasar, domin dakile yiwuwar safarar bama-bamai ko ababaen fashewa.

Sabon tsarin wanda ake sa ran fara aikinsa nan da makwanni 3, zai shafi fasinjoji akalla dubu 325 a kowace rana, wadanda ke da niyyar tasowa zuwa Amurka, wadanda zasu bi kamfanonin jiragen sama 180, daga filayen jiragen sama 280 a sassa daban daban na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.