Isa ga babban shafi
Philippines

'Yan Sandan Philippines sun kashe magajin gari da matarsa

'Yan sandan Philippines sun kai farmaki a gidan wani magajin gari da ake zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyi, in da suka kashe shi tare da matarsa da kuma wasu mutane 12.

Shugaban Philippines President Rodrigo Duterte ya lashi takobin yaki da safarar miyagun kwayoyi a kasar
Shugaban Philippines President Rodrigo Duterte ya lashi takobin yaki da safarar miyagun kwayoyi a kasar REUTERS/Ezra Acayan
Talla

Reynaldo Parojinog shi ne magajin garin Ozamiz a tsibitrin Mindanao, kuma an kashe shi ne a farmakin da ‘yan sandan suka kaddamar a gidansa.

Magajin garin dai na cikin jerin mutanen da shugaba Rodrigo Duterte ke zargi da safarar miyagun kwayoyi a kasar.

'Yan sanda a yankin sun ce, daya daga cikin masu gadin magajin garin ne ya fara bude wuta bayan sun gabatar da sammace, dalilin da ya sa ‘yan sanda suka mayar da martani.

‘Yan sandan sun ce, sun samu miyagun kwayoyi da bindigogi da kudade a samamen da suka kai gidan magajin garin.

Mutane sama da dubu 7 aka kashe tun lokacin da gwamnatin Duterte ta kaddamar da yaki da safarar miyagun kwayoyi a watan Yulin bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.