Isa ga babban shafi
Saudia

Saudiya: Daruruwan mutane sun tsere saboda rikicin Awamiya

Rahotanni daga Saudiya na cewa daruruwan mutane ne ke tserewa daga Awamiya da ke gabacin kasar bayan shafe makwanni ana rikici tsakanin jami’an tsaro da ‘yan shi’a masu dauke da makamai.

Yanzu haka kuma daruruwan mutane ne ke ficewa daga Awamiya da ke gabashin Saudiya
Yanzu haka kuma daruruwan mutane ne ke ficewa daga Awamiya da ke gabashin Saudiya Saudi News Agency/Reuters
Talla

Ana gwabza fadan ne tsakanin jami’an tsaron Saudiya da kuma wasu mabiya shi’a da suka rungumi makamai a Awamiya.

Kuma tun a watan Mayu jami’an tsaron suka kaddamar da farmaki akan ‘yan shi’ar a yankin na mabiya shi’a

Yanzu haka kuma daruruwan mutane ne ke ficewa daga Awamiya da ke gabashin kasar.

Wasu ‘yan rajin kare hakkin bil’adama sun zargi jami’an tsaron Saudiya da tursasawa mutanen yankin ficewa, saboda yadda ‘yan sanda ke harbi kan mai uwa da wabi a gidajen mutane da motoci da ke kan hanya. Da kuma katse wutar lantarki a yankin.

Akalla mutane bakwai aka kashe da suka hada da ‘yan sanda biyu a rikicin. Sannan gidaje da dama ne aka kone.

An dade dai mabiya shi’a a Saudiya na koken yadda hukumomin kasar suka yasar da su da kuma nuna masu banbanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.