Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Sabbin Takunkumai: Korea zata yi asarar $1 billion

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin Amurka na tsananta takunkumai kan Korea ta Arewa bisa gwaje-gwajenta na makami mai linzami.

MDD ta tsanantawa Korea ta Arewa Takunkumai
MDD ta tsanantawa Korea ta Arewa Takunkumai REUTERS/Toru Hanai/File Photo
Talla

Sabbin takunkuman sun hada da haramtawa Korea ta Arewa fitar da kayayyakinta zuwa kasashen ketare, abin da zai janyo ma ta asarar Dala miliyan dubu 1 a kowacce shekara.

A karon farko kenan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya dauki irin wannan mataki mai tsauri kan Korea ta Arewa tun bayan darewar shugaba Donald Trump kan karagar mulkin Amurka.

Jakadaiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta ce, daukan wannan mataki ya biyo bayan gwaje-gwajen makamai masu linzami da Korea ta yi a ‘yan kwanakin nan, abin da kasashen duniya suka yi alla-wadai da shi.

Kasar ta Korea ta kuma ce, tana da karfin kai harin da zai isa dukkanin sassan Amurka.

Daga cikin takunkuman da Kwamitin Sulhun ya kakaba wa kasar, sun hada da haramcin fitar da tama da karafa da gawayi da kifi da sauran halittun ruwa, abin da zai janyo ma ta asarar Dala miliyan dubu 1 a shekara.

Har ilya yau daga cikin abubuwan da kudirin takunkuman ya kunsa, akwai batun hana Korea ta Arewa kara adadin ma’aikatan da ta ke aika wa kasashen ketare.

Kazalika takunkuman sun hana sabbin hadin-gwiwar kasuwanci da kasar, tare da haramta zuba hannayen jari a kamfanonin hadin-gwiwar da Korea ta Arewa ke da hannu a ciki a yanzu haka.

Kwamitin ya kuma sanya takunkumi kan wasu manyan jami’an gwamnatin kasar guda tara da wasu manyan cibiyoyinta hudu da suka hada da bankinta na hada-hadar kudaden ketare.

Nikki Haley ta ce, wadanann takunkumai su ne mafi tsauri da aka taba sanya wa wata kasa a tarihin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.