rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nepal Al'adu Hakkin Mata

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nepal ta haramta kyamar mata a lokacin al’ada

media
'yammata a Nepal na shiga halin tsaka mai wuya da zarar sun kai minzalin fara jinin al'ada ta yadda ake nuna musu kyama da tsangwama baya ga tilasta musu barin gida ko kuma ware musu dakin da za su zauna har zuwa lokacin da za suyi tsarki Reuters

Majalisar kasar Nepal ta amince da wata sabuwar doka wadda ta haramta tilastawa mata barin gidajen su lokacin da suke jinin al'ada, galibi Iyaye a Nepal na tilastawa 'ya'yansu mata barin gida a lokacin da jiin al'ada ya zo musu. ita dai wannan doka ta samo assali ne daga al’adar mutanen Hindu na da.


Akasarin mutanen kasar Nepal na kallon mata masu zubar da jinin haila a matsayin marasa tsarki, kuma a wasu yankuna ma aka sanya su ne zama a wani daki na daban sabanin na auran su har sai sun yi tsarki.

Sabuwar dokar da Majalisar kasar ta amince da ita ta tanadi daurin watanni uku ko kuma biyan tarar Rupee 3,000 ko kuma Dala 30, ga duk wanda ya tilastawa wata mace bin wannan tsohuwar al’ada.

Dokar ta haramta ware mace wadda ke jinin haila ko kuma bayan ta haihu a karkashin al’adar kasar da ake kira Chhaupadi ko kuma nunawa wata mace kyama ko makamancin haka.

Kotun kolin kasar ta haramta wannan tsohuwar al’ada ce shekaru 10 da suka gabata, amma har yanzu al'umma na ci gaba da aiwatar da ita.

Sai dai wata mai kare hakkin Bil Adama, Peam Lhaki tace aiwatar da dokar zai yi matukar wahala ganin yadda mutanen kasar suka mayar da kyamar kamar addini.