Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta kada kuri'ar bunkasa shirin Nukiliya

Majalisar dokokin Iran ta kada kuri’ar amincewa da bunkasa bangaren tsaronta ta fuskar Makami mai linzami da sama da Dala Milyan dari biyar.Kudurin wanda ya samu gagarumin rinjaye na zuwa ne a matsayin martini ga takunkumin baya-bayan nan da Amurka ta kakabawa kasar bayan wani gwaijin makami mai linzami.

Majalisar dokokin Iran
Majalisar dokokin Iran Nazanin Tabatabaee Yazdi/TIMA via REUTERS
Talla

Yanzu haka dai ana jiran kada kuri’a a zagaye na biyu kan kudirin kafin amincewa ya zama doka , inda a yau ‘yan majalisu 240 daga cikin 244 suka kada kuri'ar amincewa da shi a karon Farko.

baya da kakin majalisar Ali Larijani ya sanar da sakamakon kuri'ar a zaman yau Lahadi, rahotanni sun ce an jiyo kalaman Firaiministan kasar na isar da gargadi ga Amurka, yana mai cewa matakin bunkasa bangaren makamin zai taimaka wajen kawo karshen cin kashin da Amurka ke yi a yankin gabas ta tsakiya. 

Gwamnatin Iran na da nufin sanya Dala milyan 260 don bunkasa shirye-shiryen bangaren makaminta mai linzami, inda shugaban yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da kasashen duniya Abbas Arqchi ya sanar da cewa matakin bai wargaza yarjejeniyar Iran din da kasashen duniya kan makami ta 2015 ba.

Manyan kasashen duniya irin su China da Amurka da kuma Rasha sun kulla yarjejeniya da Iran kan shirinta na kera makamin Nukiliya a wani mataki da suke ganin shi ne kadai hanyar dankwafar da kasar daga tunanin kera makamin.

Ko a makon daya gabata ma dai Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya gargadi shugaban Amurka Donald Trump kan shirin makamin na Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.